Tsallake zuwa abun ciki
Afisawa 6:1-9

Afisawa 6:1-9

1
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan.
2
Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,
3
don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
5
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi.
6
Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku.
7
Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.
8
Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.
9
Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options