Skip to content
Ayyukan Manzanni 27:17-33

Ayyukan Manzanni 27:17-33

17
Da mutanen suka jawo shi cikin babban jirgin ruwan, sai suka sa igiyoyi ta ƙarƙashin jirgin ruwan kanta don su ɗaɗɗaura shi. Don gudun kada a fyaɗa mu da yashin gaɓar Sirtis, sai suka saukar da ƙugiyar jirgin ruwan, suka bari aka yi ta tura jirgin haka.
18
Haka muka yi ta shan bugun guguwar hadarin nan kashegari suka fara jajjefar da kayan da jirgin yake ɗauke da su a cikin teku.
19
A rana ta uku, da hannuwansu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku.
20
Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.
21
Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya miƙe tsaye a gabansu ya ce, “Mutane, da kun ji shawarata na kada ku tashi daga Kirit, da ba ku fāɗa wannan masifa da hasara ba.
22
Amma yanzu ina ƙarfafa ku ku yi ƙarfin hali, domin ba ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ruwan ne kaɗai zai hallaka.
23
Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni
24
ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’
25
Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jama’a, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru.
26
Duk da haka, dole a fyaɗa mu a wani tsibiri.”
27
A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa.
28
Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in.
29
Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyin jirgin guda huɗu daga bayan jirgin suka yi fata gari ya waye.
30
Cikin ƙoƙarin tserewa daga jirgin, sai masu tuƙin jirgin suka saukar da ɗan ƙaramin jirgin ruwan cikin tekun, suka yi kamar za su saki waɗansu ƙugiyoyi daga sashen gaba na babban jirgin ne.
31
Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.”
32
Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.
33
Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options