Skip to content
Ayyukan Manzanni 20:26-38

Ayyukan Manzanni 20:26-38

26
Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina.
27
Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.
28
Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
29
Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba.
30
Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai.
31
Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.
32
“To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake.
33
Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba.
34
Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina.
35
Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
36
Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a.
37
Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba.
38
Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options