Skip to content
Ayyukan Manzanni 20:17-27

Ayyukan Manzanni 20:17-27

17
Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya.
18
Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya.
19
Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa.
20
Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida.
21
Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.
22
“Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba.
23
Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana.
24
Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.
25
“Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina.
26
Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina.
27
Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options