Skip to content
2 Sama’ila 12:24-31

2 Sama’ila 12:24-31

24
Sai Dawuda ya yi wa matarsa Batsheba ta’aziyya, ya kuma tafi wurinta ya kwana da ita. Ta kuma haifi ɗa, suka ba shi suna Solomon. Ubangiji ya ƙaunace shi;
25
kuma saboda Ubangiji ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta wurin annabi Natan yă ba shi suna Yedidiya.
26
Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin.
27
Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta.
28
Yanzu fa ka tattara saura rundunoni ka fāɗa wa birnin ka ci shi. In ba haka ba zan karɓe birnin, a kuma kira shi da sunana.”
29
Saboda haka Dawuda ya tattara sauran rundunar sojojin suka tafi Rabba suka fāɗa masa suka kuma ci shi.
30
Ya ɗauke rawanin daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti, na zinariya, an kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, aka aza shi a kan Dawuda. Ya kuma kwashe ganima mai yawa daga garin.
31
Ya fito da mutanen da suke a can, ya sa su su yi aiki da zarto, da diga, da kuma gatari, ya kuma sa su bugan bulok. Haka ya yi wa dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojoji suka koma Urushalima.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options