Skip to content
2 Sarakuna 3:6-20

2 Sarakuna 3:6-20

6
To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila.
7
Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”
8
Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?” Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”
9
Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.
10
Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Mene! Ubangiji ya kira mu sarakunan nan uku don kawai yă ba da mu ga Mowab ne?”
11
Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu nemi nufin Ubangiji ta wurinsa?” Wani hafsan sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, wanda dā ya yi wa Iliya hidima.”
12
Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.
13
Elisha ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan mahaifinka da annabawa mahaifiyarka.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “A’a, ai Ubangiji ne ya kira mu, mu sarakunan nan uku don yă bashe mu ga Mowab.”
14
Sai Elisha ya ce, “Muddin Ubangiji Maɗaukaki yana a raye, wanda nake bauta, da ba don ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuda ba, da ko kallonka ba zan yi ba.
15
Amma yanzu, a kawo mini makaɗin garaya.” Yayinda makaɗin garayan yake kiɗa, ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha
16
ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, zan cika kwarin nan da tafkunan ruwa.
17
Gama ga abin da Ubangiji ya ce, ko da yake babu iska, ko ruwan sama, duk da haka kwarin nan zai cika da ruwa, har ku da dabbobinku da kuma sauran dabbobi ku sha.
18
Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji; zai kuma ba da Mowab a gare ku.
19
Za ku ci kowane birni mai katanga, da kowane babban gari. Za ku sare kowane itace mai kyau, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku kuma yi amfani da duwatsu ku lalatar da kowace gona mai kyau.”
20
Kashegari, daidai lokacin hadaya, sai ga ruwa yana gangarowa daga gefen Edom! Ƙasar kuwa ta cika da ruwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options