2 Sarakuna 3:4-8
4
Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari.
5
Amma bayan mutuwar Ahab, sai sarkin Mowab ya yi wa sarkin Isra’ila tawaye.
6
To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila.
7
Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”
8
Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?” Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”
Settings