Skip to content
2 Sarakuna 19:27-37

2 Sarakuna 19:27-37

27
“ ‘Amma na san wurin zamanka da fitarka da shigarka da yadda kake fushi da ni.
28
Domin kana fushi da ni reninka ya iso kunnuwata, zan sa ƙugiyata a hancinka da linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma a ta hanyar da ka zo.’
29
“Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa, baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara. Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe, ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.
30
Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.
31
Gama daga Urushalima za a sami ragowa, daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.
32
“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba ko yă harba kibiya a nan. Ba zai kusace ta da garkuwa ko yă yi mata zoben yaƙi ba.
33
Ta hanyar da ya zo ne zai koma; ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.
34
Zan kāre birnin nan in cece ta, saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”
35
A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.
36
Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.
37
Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options