2 Sarakuna 17:11-21
11
Suka ƙona turare a kan kowane tudu, kamar dai yadda al’umman da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka yi muguntan da ya sa Ubangiji ya yi fushi.
12
Suka bauta wa gumaka, ko da yake Ubangiji ya ce, “Ba za ku yi wannan ba.”
13
Ubangiji ya yi wa Isra’ila da Yahuda kashedi ta bakin dukan annabawansa da kuma masu duba, cewa, “Ku juyo daga mugayen ayyukanku. Ku yi biyayya da umarnai da farillaina, bisa ga dukan Dokar da na dokaci kakanninku su bi, waɗanda na kuma bayar ta wurin bayina, annabawa.”
14
Amma ba su saurare ni ba don sun kangare kamar kakanninsu, waɗanda ba su amince da Ubangiji Allahnsu ba.
15
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.
16
Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada.
17
Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.
18
Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari,
19
ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo.
20
Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.
21
Sa’ad da ya ware Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat sarki a kansu. Yerobowam ya rinjayi Isra’ila daga ƙin Ubangiji, ya sa suka aikata babban zunubi.
Settings