2 Sarakuna 14:14-20
14
Ya kwashi ɗaukan zinariya da azurfa da duk kayan da aka samu a haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan. Ya kuma kwashi bayi sa’an nan ya koma Samariya.
15
Game da sauran ayyukan mulkin Yehowash, abin da ya yi da kuma nasarorinsa, haɗe da yaƙinsa da Amaziya sarkin Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
16
Ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Samariya tare da sarakunan Isra’ila. Yerobowam ɗansa, ya kuma gāje shi.
17
Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya yi shekaru goma sha biyar bayan mutuwar Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila.
18
Game da sauran ayyukan mulkin Amaziya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
19
Suka ƙulla masa maƙarƙashiya a Urushalima, ya gudu zuwa Lakish, amma suka aika har Lakish aka kashe shi a can.
20
Aka ɗauko shi a kan doki aka kawo shi Urushalima, aka kuwa binne shi tare da kakanninsa, a Birnin Dawuda.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings