2 Sarakuna 10:29-36
29
Duk da haka, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba, wato, yin sujada ga siffofin maruƙa na zinariya a Betel da kuma Dan.
30
Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
31
Duk da haka, Yehu bai mai da hankali ya kiyaye dokokin Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa ba. Bai rabu da zunubin Yerobowam, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.
32
A kwanakin sai Ubangiji ya fara rage girman Isra’ila, Hazayel ya yi nasara a bisa Isra’ila a ko’ina a yankinsu
33
gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan.
34
Game da sauran ayyukan mulkin Yehu, da dukan abin da ya yi, a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
35
Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa.
36
Yehu ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas.
Settings