2 Tarihi 32:1-8
1
Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa.
2
Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima,
3
sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi.
4
Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?”
5
Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.
6
Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi.
7
“Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.
8
Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.
Settings