2 Tarihi 25:14-20
14
Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa.
15
Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?”
16
Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”
17
Bayan Amaziya sarkin Yahuda ya nemi shawara mashawartansa, sai ya kalubalanci Yowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, “Zo mu gamu fuska da fuska.”
18
Amma Yowash sarkin Isra’ila ya amsa wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika da saƙo wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Sai wani naman jeji na Lebanon ya zo ya tattake ƙayar.
19
Ka ce wa kanka cewa ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana fariya da ɗaga kai. Amma tsaya dai a gida! Me ya sa kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da ta Yahuda?”
20
Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom.
Settings