Skip to content
2 Tarihi 18:1-8

2 Tarihi 18:1-8

1
Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure.
2
Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.
3
Ahab sarkin Isra’ila ya tambayi Yehoshafat sarkin Yahuda ya ce, “Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Ni kamar kai ne, kuma mutanena kamar naka ne; za mu tafi tare da kai a yaƙin.”
4
Amma Yehoshafat ya kuma ce wa sarkin Isra’ila, “Da fari mu nemi bishewar Ubangiji.”
5
Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa duka, mutane ɗari huɗu, ya kuma tambaye su, “Mu tafi yaƙi a kan Ramot Gileyad ko kada mu tafi?” Suka amsa “Tafi, gama Allah zai ba da shi cikin hannun sarki.”
6
Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”
7
Sarki Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, “Akwai guda har yanzu mai suna Mikahiya ɗan Imla, za mu iya nemi nufin Ubangiji daga gare shi, sai dai ba na sonsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai kullum masifa.” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Kada sarki yă faɗa haka.”
8
Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatansa ya ce, “A kawo Mikahiya ɗan Imla nan da nan.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options