Tsallake zuwa abun ciki
1 Timoti 6:13-21

1 Timoti 6:13-21

13
Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,
14
ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,
15
wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,
16
wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.
17
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.
18
Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako.
19
Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
20
Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,
21
wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options