1 Timoti 6:11-16
11
Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.
12
Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.
13
Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,
14
ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,
15
wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,
16
wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.
Settings