1 Timoti 1:10-20
10
da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,
11
da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.
12
Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.
13
Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.
14
An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
15
Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu.
16
Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.
17
Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
18
Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau,
19
kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.
20
Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.
Settings