Skip to content
1 Tessalonikawa 2:11-20

1 Tessalonikawa 2:11-20

11
Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa,
12
muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.
13
Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.
14
Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,
15
waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane
16
suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.
17
Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.
18
Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu.
19
Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne?
20
Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options