Skip to content
1 Sama’ila 27:7-12

1 Sama’ila 27:7-12

7
Dawuda ya zauna a yankin Filistiyawa shekara ɗaya da wata huɗu.
8
Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.)
9
Duk lokacin da ya yaƙi wani wuri, ba ya barin namiji ko mace da rai, amma sai ya kwashe tumaki, da shanu, da jakuna, da raƙuma, da riguna, sa’an nan yă koma wurin Akish.
10
Idan Akish ya ce, “Ina ka kai hari yau?” Sai Dawuda yă ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuda, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb na Keniyawa.”
11
Bai bar a kawo namiji ko mace da rai a Gat ba, gama yana tunani, “Za su ba da sanarwa a kanmu su ce, ‘Ga abin da Dawuda ya yi.’ ” Haka ya yi ta yi dukan rayuwarsa a ƙasar Filistiyawa.
12
Akish ya amince da Dawuda sosai, har ya ce wa kansa, “Ga shi ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra’ilawa, zai zama bawana har abada.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options