1 Sama’ila 24:1-7
1
Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.”
2
Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji.
3
Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon.
4
Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu.
5
Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu.
6
Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.”
7
Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa.
Settings