1 Sama’ila 23:26-29
26
Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su,
27
sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”
28
Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa.
29
Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi.
Settings