1 Sama’ila 13:1-7
1
Shawulu yana da shekara talatin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarautar Isra’ila shekara arba’in da biyu.
2
Sai ya zaɓi sojoji dubu uku daga jama’ar Isra’ila. Ya keɓe dubu biyu su kasance tare da shi a Mikmash da kuma a tuddan yankin Betel. Ya kuma bar dubu ɗaya tare da ɗansa Yonatan a Gibeya a yankin zuriyar Benyamin. Sauran sojojin kuwa Shawulu ya sallame su su koma gidajensu.
3
Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari a Geba, sai Filistiyawa suka sami labarin. Sai Shawulu ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar ya ce, “Bari Ibraniyawa su ji!”
4
Haka kuwa dukan Isra’ila suka ji labari cewa, “Shawulu ya kai hari a ƙasar Filistiyawa, yanzu Isra’ila ta zama abin ƙi ga Filistiyawa.” Aka kira mutane su haɗu da Shawulu a Gilgal.
5
Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da kekunan-dawakan yaƙi dubu talatin, da masu hawan dawakai dubu shida, da sojoji masu yawa kamar yashi a bakin teku. Suka tafi Mikmash a gabashin Bet-Awen, suka kafa sansani a can.
6
Sa’ad da Filistiyawa suka fāɗa wa Isra’ilawa da yaƙi mai tsanani, suka sa su cikin wani hali mai wuya, sai Isra’ilawa suka ɓuya a kogwanni, da ciyayi, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi.
7
Waɗansunsu ma suka haye Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Shawulu ya zauna Gilgal, dukan ƙungiyoyi sojojin da suke tare da shi suka yi rawan jiki don tsoro.
Settings