Skip to content
1 Sarakuna 6:1-8

1 Sarakuna 6:1-8

1
A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.
2
Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne.
3
Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma.
4
Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin.
5
A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe.
6
Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali.
7
A yin ginin haikalin, duwatsun da aka fafe ne kaɗai daga wurin fafe duwatsu aka yi amfani da su, ba a ji karar guduma ko gizago, ko wani abin da aka yi da ƙarfe a wurin ginin haikali yayinda ake gina shi ba.
8
Ƙofar zuwa ɗakunan ƙasa tana gefen kudu na haikalin; akwai matakai da suka bi zuwa hawa na tsakiya, daga can kuma matakan sun wuce zuwa hawa na uku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options