1 Sarakuna 22:41-50
41
Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarkin Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra’ila.
42
Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa, Azuba ’yar Shilhi.
43
A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can.
44
Yehoshafat kuma ya zauna lafiya da sarkin Isra’ila.
45
Game da sauran ayyukan mulkin Yehoshafat da abubuwan da ya yi, da kuma yaƙe-yaƙensa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
46
Ya kawar da karuwai maza na masujadai da suke kan tuddai waɗanda suka rage tun mulkin mahaifinsa Asa.
47
Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki.
48
To, Yehoshafat ya gina jerin jiragen ruwan kasuwanci don su je Ofir saboda zinariya, amma ba su yi tafiya ba, gama sun farfashe a Eziyon Geber.
49
A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi.
50
Yehoshafat kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin Dawuda kakansa. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi.
Settings