1 Sarakuna 20:21-34
21
Sarki Isra’ila ya bi, ya kuma sha ƙarfin dawakan da keken yaƙin, ya kashe Arameyawa da yawa.
22
Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.”
23
Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi.
24
Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu.
25
Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka.
26
Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila.
27
Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.
28
Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”
29
Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya.
30
Sauransu suka tsere zuwa birnin Afek, inda katangar ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai. Sai Ben-Hadad ya gudu zuwa birni ya ɓuya a ciki cikin ɗaki.
31
Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.”
32
Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”
33
Da ma abin da fadawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad!” Sarki ya ce, “Ku je ku kawo shi.” Da Ben-Hadad ya fita, sai Ahab ya sa aka kawo shi cikin keken yaƙinsa.
34
Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi.
Settings