Tsallake zuwa abun ciki
1 Korintiyawa 16:5-9

Shirye-shiryen tafiyar Bulus

1 Korintiyawa 16:5-9
5
Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya.
6
Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni.
7
Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda.
8
Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos,
9
domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options