1 Tarihi 4:4-23
4
Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem.
5
Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara.
6
Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara.
7
’Ya’yan Hela maza su ne, Zeret, Zohar, Etnan,
8
da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
9
Yabez ya fi ’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.”
10
Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.
11
Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.
12
Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka.
13
’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya. ’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai.
14
Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne.
15
’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne, Iru, Ela da Na’am. Ɗan Ela shi ne, Kenaz.
16
’Ya’yan Yahallelel su ne, Zif, Zifa, Tiriya da Asarel.
17
’Ya’yan Ezra maza su ne, Yeter, Mered, Efer da Yalon. Ɗaya daga cikin matan Mered ta haifi Miriyam, Shammai da Ishba wanda ya haifi Eshtemowa.
18
(Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne ’ya’yan Bitiya ’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura.
19
’Ya’yan matar Hodiya, ’yar’uwar Naham su ne, suka haifi Keyila Bagarme, da Eshtemowa mutumin Ma’aka.
20
’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet.
21
’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya,
22
da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.)
23
Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki.
Settings