Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ziklag
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ziklag, Madmanna, Sansanna,
Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,
Sai Dawuda ya ce wa Akish, “In na sami tagomashi a gabanka ka ba ni wani wuri a cikin biranenka in zauna a can. Don me bawanka zai kasance tare da kai a gidan sarauta?”
A ranar Akish ya ba shi Ziklag wanda tun dā take ta sarkin Yahuda.
Bayan mutuwar Shawulu, Dawuda ya dawo daga karkashe Amalekawa. Sai ya zauna a Ziklag kwana biyu.
Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi;
Akwai su a Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta.