Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wolf: Ravenous

5 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da Ravenous

  1. “Benyamin kyarkeci ne mai kisa; da safe yakan cinye abin da ya farauto da yamma yakan raba ganima.”

  2. Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa.

  3. Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba.

  4. Sarakunanki ruri ne na zakoki, shugabanninki kyarketan dare ne, waɗanda ba sa rage kome don safe.

  5. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.