Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vinegar

9 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.

  2. A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.

  3. Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.

  4. Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.

  5. Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.

  6. A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.

  7. Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha.

  8. Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.

  9. To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu.