Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Uzzi

11 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi,

  2. Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot,

  3. Bukki, Uzzi, Zerahiya,

  4. ’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600.

  5. Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya. ’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne.

  6. ’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034.

  7. Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya.

  8. ɗan Zerahiya, ɗan Uzzi, ɗan Bukki,

  9. Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.

  10. na iyalin Yohiyarib, Mattenai; na iyalin Yedahiya, Uzzi;

  11. haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya.