Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thistle

6 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona.

  2. Amma Yehowash sarkin Isra’ila ya mai da martani wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ’yar ƙaya a kurmin Lebanon ta aika da saƙo wurin itacen al’ul a Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Amma wani naman jeji ya zo ya tattake ƙayar.

  3. Amma Yowash sarkin Isra’ila ya amsa wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika da saƙo wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Sai wani naman jeji na Lebanon ya zo ya tattake ƙayar.

  4. bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.

  5. Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”

  6. Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?