Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thessalonica: People of, persecute Paul

6 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da People of, persecute Paul

  1. Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron.

  2. Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan,

  3. Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”

  4. Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi.

  5. Bereyawa kuwa sun fi Tessalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne.

  6. Da Yahudawan da suke a Tessalonika suka ji cewa Bulus yana wa’azin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma tā da hankalinsu.