Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Macedonian Empire: The little horn to arise out of one of its divisions

8 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da The little horn to arise out of one of its divisions

  1. Bunsurun kuwa ya ƙasaita, amma a ƙwanƙolin ikonsa sai aka karye babban ƙahonsa, kuma a wurin da ƙahon nan ya kasance waɗansu sanannun ƙahoni huɗu suka tsiro suna fuskantar kusurwoyin nan huɗu.

  2. Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa.

  3. Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su.

  4. Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa.

  5. Saboda tawaye, sai aka ba da rundunar tsarkaka da kuma hadayar ƙonawa ta kowace rana ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara.

  6. “Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito.

  7. Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka.

  8. Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.