Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Locust: Of destructive enemies

8 ayoyi · 19 fannoni

Ayoyi game da Of destructive enemies

  1. rana ce ta baƙin duhu ƙirin, ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa kamar ketowar alfijir a kan duwatsu yadda ba a taɓa ganin irinta ba, ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa.

  2. A gabansu wuta tana ci, a bayansu ga harshen wuta yana ci, A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden, a bayansu kuma jeji ne wofi, babu abin da ya kuɓuce musu.

  3. Suna da kamannin dawakai; suna gudu kamar dokin yaƙi.

  4. Da motsi kamar na kekunan yaƙi sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu, kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka, kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.

  5. Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba; kowace fuska ta yanƙwane.

  6. Sukan auka kamar jarumawa; sukan hau katanga kamar sojoji. Kowa yana takawa bisa ga tsari, ba mai kaucewa.

  7. Ba sa turin juna, kowane yakan miƙe gaba. Sukan kutsa cikin abokan gāba ba mai tsai da su.

  8. Sukan ruga cikin birni, suna gudu a kan katanga. Sukan hau gidaje, sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.