Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Humility of Christ: Saints should imitate

4 ayoyi · 20 fannoni

Ayoyi game da Saints should imitate

  1. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

  2. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

  3. amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.

  4. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!