Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Excellency and Glory of Christ: As King

5 ayoyi · 40 fannoni

Ayoyi game da As King

  1. A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali.

  2. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi.

  3. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

  4. Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

  5. Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”