Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tears: Observed by God
Ayoyi game da Observed by God
Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
“Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa,
“Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.