Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Students

8 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai ya aiki mutane su je su kamo Dawuda, amma da suka ga ƙungiyar annabawa suna annabci tare da Sama’ila shugabansu a tsaye, sai Ruhun Allah ya sauko wa mutanen Shawulu, su ma suka fara yin annabci.

  2. Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi.

  3. Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel.

  4. Sai ƙungiyar annabawa a Betel suka fito zuwa wajen Elisha suka ce masa, “Ka san cewa Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga wurinka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma kada ku yi magana game da wannan.”

  5. Ƙungiyar annabawa a Yeriko suka haura zuwa wajen Elisha suka ce, “Ko ka san Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga gare ka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma ku bar zancen nan tukuna.”

  6. Mutum hamsin na ƙungiyar annabawa suka je suka tsaya da nisa, suna fuskantar inda Iliya da Elisha suka tsaya a Urdun.

  7. Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa.

  8. Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”