Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Science

16 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.

  2. Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.

  3. Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,

  4. ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.

  5. Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.

  6. Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.

  7. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.

  8. Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”

  9. Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane!

  10. Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.

  11. Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba; ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.

  12. Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.”

  13. Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.

  14. “Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”

  15. mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya

  16. Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,