Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Poverty

12 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.

  2. Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci.

  3. Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.

  4. Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.

  5. Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.

  6. gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  7. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,

  8. sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.

  9. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.

  10. Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

  11. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

  12. Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai da tafin hannu biyu cike da tashin hankali da harbin iska kawai.