Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pottery

7 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo, wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana. Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya, sai ka ce maginin tukwane yana taka laka.

  2. Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen.

  3. Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.

  4. Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi.

  5. Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau.

  6. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa,

  7. suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”