Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Post: Of Hezekiah
Ayoyi game da Of Hezekiah
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.
’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a.