Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Personal Call

13 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani.

  2. Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su.

  3. kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,

  4. “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam.

  5. Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi.

  6. Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.

  7. “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsufantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;

  8. suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u;

  9. suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’

  10. “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.

  11. Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.

  12. Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka

  13. har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?