Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pen

7 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Waɗansu suka zo daga Efraim, waɗanda ainihinsu daga Amalek ne; Benyamin yana tare da mutanen da suka bi ka. Daga Makir, shugabannin sojoji suka gangaro, daga Zebulun waɗanda suke riƙe da sandan komanda suka fito.

  2. a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada!

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Lili.” Na ’ya’yan Kora maza. Maskil Waƙar Aure. Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.

  4. Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.

  5. “ ‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima, gama muna da dokar Ubangiji,” alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda ya yi ƙarya?

  6. “An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu.

  7. Ina da abubuwa da dama da zan rubuta maka, sai dai ba na so in yi amfani da alƙalami da inki in rubuta su.