Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Onyx

14 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.)

  2. da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  3. “Ka ɗauki duwatsu biyu masu daraja, ka rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kai

  4. bisa ga haihuwarsu, sunaye shida a kan dutse ɗaya, saura shida kuma a kan ɗaya dutsen.

  5. A rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsu biyun, yadda mai yin aiki da dutse mai daraja yakan zāna hatimi. Sa’an nan a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya

  6. a ɗaura su a kan ƙyallen kafaɗa efod a matsayin duwatsun tuni ga ’ya’yan Isra’ila. Haruna ne zai ɗauki sunayen a kafaɗarsa don tuni a gaban Ubangiji.

  7. A jeri na huɗu, a sa kirisolit, da onis, da yasfa. Ka sa su a tsaiko na zinariya.

  8. duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  9. Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.

  10. a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.

  11. Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.

  12. Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.

  13. Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su.

  14. na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis.