Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Justification Before God: Is of grace

5 ayoyi · 24 fannoni

Ayoyi game da Is of grace

  1. Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.

  2. Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane.

  3. Gama kamar yadda ta wurin rashin biyayyar mutum guda, mutane masu yawa suka zama masu zunubi, haka kuma ta wurin biyayyar mutum guda, mutane da yawa za su zama masu adalci.

  4. An ba da dokar don mu ga yadda laifi yake da girma. Amma da zunubi ya ƙaru, sai alheri ya ƙaru sosai,

  5. domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.