Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idol: Manufacture of

8 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Manufacture of

  1. Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa, maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.

  2. Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.

  3. Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya.

  4. Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki, waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?

  5. Shi da irinsa za su sha kunya; masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum. Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu; za su firgita su kuma sha mummunan kunya.

  6. Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki ya yi aiki da shi a cikin garwashi; ya ƙera gunki da guduma, ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi. Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi; yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.

  7. Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba.

  8. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a.