Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Fish: Clean and unclean

6 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Clean and unclean

  1. “ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.

  2. Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.

  3. Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu.

  4. Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.

  5. Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki.

  6. Amma duk wani abin da ba shi da ƙege da ɓamɓaroki, ba za ku ci ba; gama marar tsarki ne gare ku.