Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Father-in-Law: Unjust, Laban to Jacob

7 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Unjust, Laban to Jacob

  1. Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”

  2. Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki.

  3. Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita.

  4. Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare.

  5. Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci.

  6. Haka ya kasance shekaru ashirin da na yi a gidanka. Na yi maka aiki shekaru goma sha huɗu domin ’ya’yanka mata biyu, na kuma yi shekaru shida domin garkunanka, ka kuma canja albashina sau goma.

  7. Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”